Isa ga babban shafi

Kawancen yammacin Turai sun ce za su kare sararin samaniyar Ukraine

Kasashen yammacin duniya da ke goyon bayan Ukraine, sun tattauna kan yadda za su samar da karin matakan kariya ta sama zuwa Kyiv, yayin da Washington ta ce matakan da Rasha ta dauka na baya-bayan nan ne suka tilastawa kasashen kawance taikamawa kasar.

Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO kenan, Jens Stoltenberg
Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO kenan, Jens Stoltenberg AP - Virginia Mayo
Talla

Ministan tsaron Ukraine Oleksiy Reznikov ya shaidawa zauren taron da aka yi a hedkwatar NATO da ke Brussels cewa kasarsa na bukatar taimakon sararin samaniya.

Kungiyar kasashe kusan 50 karkashin jagorancin Amurka na tattaunawa a hedkwatar kungiyar tsaro ta NATO da ke Brussels tare da mayar da hankali kan tsaro ta sama bayan da Rasha ta yi ruwan bama-bamai a Ukraine bayan fashewar wani abu a wata gada da ke gabar tekun Crimea.

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi kira ga shugabannin G7 a ranar Talata da su taimaka wajen samar da tsaron sama a kan kasarsa.

Shugaban kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ce tattaunawar za ta duba batun yadda za a kara kaimi ga Ukraine kuma babban abin da zai sa a gaba shi ne samar da tsaro ta sama bayan hare-haren na wannan mako.

Kawancen kasashen yamma sun yi ta kokarin samar da hanyoyin samar da ci gaba ga Ukraine kamar yadda jami'an diflomasiyya suka yarda cewa suna da 'yan tsiraru da za su taimakawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.