Masu zanga-zanga 92 aka kashe a kasar Iran - Bincike
Akalla mutane 92 ne aka kashe a kasar Iran sakamakon murkushe masu zanga-zanga, makonni biyu da barkewarta bayan mutuwar Mahsa Amini a hannun ‘yan sandan da suka kama ta.
Wallafawa ranar:
Wata sanarwa da kungiyar kare hakkin bil'adama mai hedkwata a kasar Norway ta fitar, ta ce shakka babu an ci zarafin masu zanga-zanga a kasar ta Iran
Daraktan kungiyar a Iran, Mahmood Amiry-Moghaddam, ya ce hukumomin kasa da kasa na da alhakin gudanar da bincike kan wannan laifi da kuma hana ci gaba da aikata laifuka daga a kasar.
Alkaluman da aka fitar na baya-bayan nan, sun ce an tabbatar da kashe mutane 83 a zanga-zangar kasar Iran.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu