Isa ga babban shafi

An tara sama da dala biliyan 14 don yaki da cutukan HIV, tarin fuka

Asusun Duniya na Yaki da Cutar Kanjamau, tarin fuka da kuma zazzabin cizon sauro ya tara dala biliyan 14.25 jiya Laraba, a taron bayar da agajin da ya gudana karkashin jagorancin shugaban kasar Amurka Joe Biden.

Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz  a taron Gidauniyar duniyar a birnin new York ranar 21 ga Satumba, 2022.
Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz a taron Gidauniyar duniyar a birnin new York ranar 21 ga Satumba, 2022. AP - Evan Vucci
Talla

Wannan shi ne mafi girman adadin kudaden tallafin da aka yi alkawarin samarwa, duk da cewar na gaza cimma burin da ake da shi na tara dala biliyan 18 bayan Burtaniya da Italiya suka ce za su sanar da nasu tallafin daga baya.

Amurka dai ta yi alkawarin bayar da mafi girman tallafin da ya kai dala biliyan 6, sai Faransa da ta biya Euro biliyan 1.6, Jamus ta ba da Euro biliyan 1.3, da kuma Japan mai dala biliyan 1.08.

Makasudin burin tara wadannan kudade har dala biliyaan 18 shine dawowa kan hanya a game da yaki da cutar hiv mai karya garkuwar jiki, tarin fuka da malaria zuwa shekarar 2030, wanda aka samu koma baya sakamakon bullar annobar Covid -19.

An samar da wannan gidauniya ce a shekarar 2002, wadda ta hada kan gwamnatoci, kungiyoyi da hukumomi da kungiyoyin fararen hula da zummar yaki da wadannan cutuka da suka addabi duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.