Isa ga babban shafi

An cimma yarjejeniyar rabon magungunan rage yaduwar HIV masu rahusa

Kungiyar UNAIDS ta cimma yarjejeniyar rabon wasu magunguna da masu fama da cuta mai karya garkuwar jiki ke amfani da shi, musamman ga kasashe masu fama da talauci don rage kaifinta da kuma yadda take yaduwa cikin sauri.

Akalla mutane miliyan 38na rayuwa da cutar HIV. a 2019, a cewar UNAIDS.
Akalla mutane miliyan 38na rayuwa da cutar HIV. a 2019, a cewar UNAIDS. AFP/File
Talla

A taron da kungiyar ta gudanar da birnin Motreal na Canada kungiyar ta ce kasashen ‘yan rabbana ka wadata mu sune kan gaba wajen fama da yaduwar cutar, don haka sune za’a fi tallafawa da magunguna cutar masu saukin kudi da saukin adanawa.

Yarjejeniyar da aka kulla da kamfanin samanr da magunguna na ViiV Healthcare na Birtaniya zata bai wa kamfanonin samar da magunguna damar shigar da magungunan a wasu nahiyar Africa.

Haka kuma yarjejeniyar ta amince a samar da allurar  saukaka kaifin cutar, samfurin Cobotegravis, wadda ke da juriya da kuma dadea a wajen adanawa, kuma za’a shigar da ita kasashe 90 a fadin duniya.

Kulla yarjejeniyar dai na zuwa ne sakamakon fargabar da majalisar dinkin duniya ta nuna game da yadda yaki da cutar ke cikin hadari, la’akari da yadda hankalin hukumomi ke kan yakin Russiada Ukraine yayin da wasu kasashen suka mayar da hankali wajen yaki da ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.