Isa ga babban shafi

Kotun Faransa ta ci tarar jirgin da ya yi sakacin kashe fasinjojinsa

Wata Kotun birnin Paris da ke Faransa ta samu jirgin sama na kasar Yemen da laifin salwantar da rayukan fasinjojinsa ba da gan-gan ba bayan ya yi hatsari a shekarar 2009.

Wani bangare na jirgin Yemenia Airways da ya yi hatsari a 2009 a tekun India.
Wani bangare na jirgin Yemenia Airways da ya yi hatsari a 2009 a tekun India. AFP - IBRAHIM YOUSSOUF
Talla

Kotun ta birnin Paris ta ci tarar jirgin na Yemenia Airways Euro dubu 225, sannan ta umarci kamfanin jirgin da ya biya Euro miliyan guda ga dangin fasinjojin.

Koda yake shugabannin kamfanin jirgin saman na Yemenia Airways ba su halarci zaman shari’ar ba, inda suka kafa hanzari da yakin basasar da ake fama da shi a kasarsu.

Jirgin dai ya taso ne a ranar 29 ga watan Yunin shekarar 2009 daga babban brinin Yemen Sanaa zuwa Comoros dauke da fasinjoji 142, kuma 66 daga cikinsu Faransawa ne, yayin da ya yi hstari a tekun India, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar daukacin mutanen da ke cikinsa, in ban da wata yarinya mai shekaru 12 da ta tsira da ranta a wancan lokacin.

Masu bincike da kwararru sun gano cewa, babu wata matsalar tattare da jirgin lokacin da ya yi hatsarin, amma sun dora alhakin aukuwar hatsarin kan rashin kwarewar da ma’aikatansa suka nuna a daidai lokacin da suke tunkarar babban birnin Moroni na Comoros cikin dare.

Kazalika masu shigar da kara na gwamnati sun caccaki kamfanin kan yadda ya bari jirgin ya tashi cikin dare duk da cewa, wasu daga cikin fitulunsa ba sa aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.