Isa ga babban shafi

EU na duba yuwuwar magance matsalar yadda ake barnar makamashi

Shugabar kungiyar Tarayyar Turai ta EU Ursula von der Leyen ta yi kira da a rage amfani da wutar lantarki a dukkanin kasashe mambobin kungiyar tare da rage harajin iska kan kamfanonin makamashi don magance tsadar kayayyaki.

Bututun mai na Nord Stream 2 a Ust-Luga na kasar Rasha wanda zai aka so amfaqni da shi wajen isar da iskar gas zuwa Turai kafin a soke batun sakamakon mamayar da Moscow ta yi wa Ukraine.
Bututun mai na Nord Stream 2 a Ust-Luga na kasar Rasha wanda zai aka so amfaqni da shi wajen isar da iskar gas zuwa Turai kafin a soke batun sakamakon mamayar da Moscow ta yi wa Ukraine. © Andrey Rudakov/Bloomberg
Talla

Shugabar wadda ta shaidawa Majalisar Tarayyar Turai cewa farashin iskar gas da wutar lantarki ya yi tashin gwauron zabi bayan da Rasha ta mamaye Ukraine, ta ce ya kamata a rage amfani da lantarki akalla ko da kashi biyar ne.

Sai dai an dakatar da tsare-tsare kan farashin iskar gas, wanda ya kasance wani muhimmin abin da Rasha ke fitarwa zuwa Tarayyar Turai.

Kasashe mambobin kungiyar EU za su yi tsokaci kan shawarwarin tare da fatan cimma yarjejeniya a karshen wannan wata.

Von der Leyen ta kuma sanar da cewa za ta sake ziyartar Ukraine domin tattaunawa da shugaba Volodymyr Zelensky, tana mai cewa: "Turai za ta ci gaba da nuna goyon bayanta ga Ukraine."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.