Isa ga babban shafi

Indonesia na son taron G20 ya cimma matsaya kan yaki da sauyin yanayi

Indonesia da ke shirin karbar bakonci kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki ta bukaci shugabannin kasashe da kungiyoyin da za su halarci taron su mayar da hankali don daukar matakan da suka kamata wajen yaki da dumammar yanayi, la’akari da yadda tuni aka fara ganin illar gaza daukar matakin magance matsalar.

Wani bangare na shirye-shiryen karbar bakoncin taron G20.
Wani bangare na shirye-shiryen karbar bakoncin taron G20. © Made Nagi/Poll via REUTERS
Talla

Kiran na Indonesia yayin taron yini guda a tsibirin Bali na zuwa ne a dai dai lokacin da mutane fiye da dubu daya da dari daya suka mutu a Pakistan sanadiyyar ambaliyar ruwa da ake alakantawa da sauyin yanayi.

Baya ga ambaliyar ruwan ke ci gaba da tsananta a wasu sassa na Duniya itama China ta samu tsananin zafi fiye da yadda ta ke gani haka zalika wasu sassa na Turai.

Ministar muhalli na Indonesia Siti Nurbaya Bakar ta ce wajibi ne a dauki matakan da suka dace yayin taron na G20 don ceto Duniya daga fadawa barazana.

A cewar ministar matsalar dumamar yanayi ba kadai ci gaban da kassahe suka cimma za su rushe ba, ba za su bayar da damar gina goben yaran da za su taso a nan gaba ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.