Isa ga babban shafi

Putin da Xi sun ba da tabbacin halartar taron G20 da zai gudana a Indonesia

Shugaba Joko Widodo na Indonesia ya tabbatar da cewa shugabannin kasashen Rasha Vladimir Putin da na China Xi Jinping za su halarci taron G20 da zai gudana a Bali cikin watan Nuwamba mai zuwa, duk da jita-jitar yiwuwar a haramta musu zuwa taron.

Shugaba Xi Jinping na China da Vladimir Putin na Rasha.
Shugaba Xi Jinping na China da Vladimir Putin na Rasha. AP - Alexei Druzhinin
Talla

A zantawarsa da Bloomberg shugaba Jokowi ya ce Putin da Xi dukkaninsa sun bashi tabbacin halartar taron wanda kasarsa za ta karbi bakonci a tsibirin Bali.

Ma’aikatar harkokin wajen China dai ba ta bayar da tabbacin yiwuwar zuwan shugaba Xi taron ba, haka zalika ofishin shugaban kasar Indonesia bai amsa tambayoyin Reuters kan manyan baki da za su halarci taron na watan Nuwamba ba.

Indonesia na shirin karbar bakoncin kasashen 20 ne mafiya karfin tattalin arziki a wani yanayi da kasar ke fuskantar matsin lamba daga kasashen yammaci don ganin ta janye gayyatar da ta yiwa shugaba Vladimir Putin na Rasha saboda mamayar da yak e a Ukraine wadda ya kira da atisayen Soji na musamman.

Sai dai shigaba Jokowi, ya ce dukkanin kasashen biyu na kallonshi a matsayin mai shiga tsakani bayan da ya gana da shugaba Putin da kuma Zelensky na Ukraine.

Shugabannin kasashe ciki har da Joe Biden na Amurka ake sa ran s hallara a tsibirin na Bali da ke Indonesia cikin watan Nuwamba taron da kuma a wannan karon zai samu halartar Volodymyr Zelensky.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.