Isa ga babban shafi
Japan-G20

Taron G20 ya kankama a birnin Osaka na Japan

An shiga rana ta biyu da fara taron kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki a duniya da ke gudana can a birnin Osaka na Japan, sai dai an rufe rana ta farko ba tare da kammala tattaunawa kan batutuwan da aka tsammaci su za su mamaye taron ba.

Shugabannin kasashen duniya yayin taron G20 a birnin Osaka na Japan
Shugabannin kasashen duniya yayin taron G20 a birnin Osaka na Japan Brendan Smialowski / AFP
Talla

Taron wanda ya faro daga jiya juma’a da ke samun halartar manyan kasashen duniya, ya mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi kimiyyar zamani, inda aka gano shugaba Donald Trump na Amurka da Vladimir Putin na Rasha na raha da juna duk kuwa da jita-jitar tsamin alaka tsakanin manyan shugabannin biyu.

A bangare guda yayin kebantaccen taron da shugabannin Amurka da China, su ka gudanar a safiyar yau Asabar, sun amince da sake kulla wata sabuwar yarjejeniyar kasuwanci tsakaninsu a wani yunkurin na kawo karshen yakin kasuwancin da ke tsakaninsu.

Jaridar Chinan Xinhua ta ruwaito shugaban kasar Xi Jinping na cewa Donald Trump ya janye matakinsa na sake sanya haraji kan wasu kayaki da Beijing ke shigarwa kasar.

Ita kuwa a nata bangaren shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel cewa ta yi akwai bukatar kasashen 20 su amince da fara amfani da sharuddan da ke kunshe cikin yarjejeniyar yanayi ta Paris, ko da dai Amurka na ci gaba da kayracewa matakin.

Yanzu haka dai kasashe 19 cikin 20 ban da Amurka da ke halartar taron su amince da sanya hannu don fara amfani da dokokin da yarjejeniyar ta kunsa.

Amurka dai ta sake nuna halin ko'in kula kan yarjejeniyar kamar dai yadda ta yayin makamancin taron da ya gudana a Argentina cikin watan Disamban bara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.