Isa ga babban shafi

Pakistan ta fuskanci ambaliya mafi muni da ba a taba gani ba - Minista

Gwamnatin Kasar Pakistan tace yanzu haka ambaliya sakamakon ruwan saman da ake shatatawa a kasar tun daga tsakiyar watan Yuni ya mamaye kashi guda bisa uku na fadin kasar.

Wasu mutane kenan da suka rasa matsugunansu dauke da kayayyaki bayan da a kokarin gujewa ambaliyar da ta afkawa gidajensu dake Jaffarabad, gundumar lardin Baluchistan da ke kudu maso yammacin Pakistan.
Wasu mutane kenan da suka rasa matsugunansu dauke da kayayyaki bayan da a kokarin gujewa ambaliyar da ta afkawa gidajensu dake Jaffarabad, gundumar lardin Baluchistan da ke kudu maso yammacin Pakistan. AP - Zahid Hussain
Talla

Ministar kula da sauyin yanayi Sherry Rehman tace ambaliyar ta shafi mutane akalla miliyan 33, abinda ake dangantawa da mutuum guda a cikin mutane bakwai dake cikin kasar, yayin da wadanda suka mutu suka haura 1,136.

Rahotanni sun ce ruwan da ya malala ya mamaye daukacin gonakin dake kudancin Yankin Sindh da Yammacin Balochistan, yayin da ya wanke hanyoyi da gadajen dake arewacin kasar.

Rehman tace ganin ambaliyar kan shi tashin hankalin, ballantana irin illar da yayi na rusa gidaje da mamaye gonaki da kashe dabbobi.

Ministar ta kuma bayyana fargabar cewar, adadin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar zai tashi, domin kuwa yanzu haka akwai wurare da dama dake yankin arewacin Pakistan wadanda hanyoyin zuwa wuran sun katse.

Rehman ta sake daga muryar ta domin neman taimakon kasashen duniya danganer da wannan iftila’in da ya afakawa mutanen kasar, yayin da take zargin manyan kasashen duniya da haifar da matsalar sauyin yanayin da ya shafe su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.