Isa ga babban shafi

EU: Iran ta bukaci a gabatar mata da sabon daftarin yarjejeniyar nukiliya

Iran ta bukaci Kungiyar Tarayyar Turai, ta yi wa sabon daftarin yarjejeniyar nukliyar da ta gabatar mata gyaran fuska, a wani yunkuri na sake farfado da yarjejeniyar da aka kulla a shekarar 2015.

Kasashen Turai dai na zargin Iran da  ci gaba da kera makaman nukiliya, zargin da kasar ke musantawa
Kasashen Turai dai na zargin Iran da ci gaba da kera makaman nukiliya, zargin da kasar ke musantawa AFP - HANDOUT
Talla

Babban jami’in diflomsiyar Kungiyar, Josep Borrell ya ce akasari kasashen dake da hannu a yarjejeniyar nukliya da Iran, sun aminta da sabon daftarin banda Amurka da kawo yanzu bata bayyana matsayarta a kai ba.

Sai dai bayan shafe tsawon shekara guda ba tare da an gudanar da tattaunawa ba, a farkon watan nan ne, EU ta gabatar da daftarinta na karshe dangane da sabuwar yarjejeniyar da za’a kulla.

Yarjejeniyar nukliyar da aka kulla cikin shekarar 2015 tsakanin Iran da Britaniya, da China, da Faransa, da Jamus da Rasha da kuma Amurka, ta rushe saboda abin da Amurka ta kira na rashin mutunta ta.

An dai kulla yarjejeniyar ne lokacin tsohon shugaban Amurka, Barrack Obama bayan hana Iran kera  makaman nukiliya, wani abu da ta dade tana muradi a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.