Isa ga babban shafi

Isra'ila da Turkiyya za su maido da alakar diflomasiyya

Isra'ila da Turkiyya sun sanar da shirin gyara alakarsu ta huldar diflomasiyya, biyo bayan tsawon shekaru da tabarbarewar alaka tsakanin kasashen da ke yankin tekun Meditariniya

Kasashen na son inganta alakar diplomasiyya domin inganta tattalin arziki
Kasashen na son inganta alakar diplomasiyya domin inganta tattalin arziki © daily sabah
Talla

Firaministan Isra'ila Yair Lapid, ya yaba da ci gaban diflomasiyya a matsayin zaman lafiyar yankin da kuma labarai masu matukar muhimmanci ga 'yan kasar Isra'ila.

Ofishin Lapid ya ce ci a gaban diflomasiyya za a sake aikewa da jakadu zuwa ofishin jakadancin kasashen biyu.

Sanarwar ta biyo bayan kokarin da kasashen biyu suka kwashe watanni suna yi na gyara alakar da ke tsakaninsu, inda manyan jami'an kasar suka kai ziyara ga juna.

Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu, ya ce komawar jakadun yana da matukar muhimmanci wajen inganta alakar da ke tsakanin kasashen biyu, yayin da ya sha alwashin kare hakkin Falasdinu.

Cavusoglu a watan Mayu ya zama ministan harkokin wajen Turkiyya na farko da ya ziyarci Isra'ila a cikin shekaru 15, a ziyarar da ya kai wanda kuma ya gana da shugabannin Falasdinawa a yammacin gabar kogin Jordan.

A wata muhimmiyar ziyara da shugaban kasar Isra'ila Isaac Herzog ya kai birnin Ankara na kasar Turkiyya watanni biyu da suka gabata, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana ganawar tasu ta zama wani muhimmin lokaci ga alakar kasashen biyu.

Dangantakar kasashen biyu ta fara tsami ne a shekara ta 2008, bayan wani farmakin da sojojin Isra'ila suka kai a Gaza.

A shekarar 2010 dangantaka ta yi tsami bayan mutuwar fararen hula 10 sakamakon wani samame da Isra'ila ta kai kan jirgin ruwan Mavi Marmara na Turkiyya, wani bangare na wani jirgin ruwan da ke kokarin keta wa domin kai kayan agaji zuwa Gaza.

An dai gudanar da wani dan takaitaccen sulhu ne daga shekarar 2016 zuwa 2018, lokacin da Turkiyya ta janye jakadanta tare da korar Isra'ila saboda kashe Falasdinawa. Sama da 'yan Gaza 200 ne sojojin Isra'ila suka harbe a lokacin zanga-zangar kan iyaka daga 2018 zuwa 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.