Isa ga babban shafi

An kashe mutane 11 a harin da Turkiyya ta kai kan iyakar Siriya

Jiragen yakin saman Turkiyya sun yi luguden wuta kan iyakar Siriya da ke karkashin ikon dakarun gwamnati, inda suka kashe mutane 11, bayan wani artabu da aka yi cikin dare tsakanin dakarun Ankara da mayakan Kurdawa da ke iko da yankin.

Shugaba Tayyip Erdogan, na turkiyya kenan
Shugaba Tayyip Erdogan, na turkiyya kenan via REUTERS - MURAT CETINMUHURDAR/PPO
Talla

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Siriya, ta ce mayaka 11 aka kashe, said ai bata bayyana cewa ko wadanda aka kashen na da alaka da gwamnatin Damascus ko kuma dakarun Kurdawa ba.

Dakarun Syrian Democratic Forces karkashin jagorancin Kurdawa sun bayyana cewa, jiragen yakin Turkiyya sun kai hare-hare 12 a kan sansanonin sojojin Syria da aka jibge a kan iyakar kasar da yammacin Kobane, garin da Kurdawa ke rike da shi.

An dai jibge dakarun gwamnatin Siriya a yankunan da mayakan Kurdawa ke iko wanda ke kusa da kan iyakar Turkiyya a wani bangare na yarjejeniyoyin da aka cimma kan yadda za a dakile hare-haren wuce gona da iri da Syria ke kaiwa dakarun Kurdawa da take kallo a matsayin 'yan ta'adda.

Kungiyar da ke sanya idanu a Syria ta Birtaniya, ta ce hare-haren ya biyo bayan arangamar da aka yi cikin dare tsakanin dakarun Ankara da na SDF karkashin jagorancin Kurdawa a yammacin Kobane.

A wani bangare na ci gaba da kai hare-hare, dakarun Kurdawa sun kai farmaki a cikin yankin na Turkiyya, inda suka kashe soja guda.

Tun a shekara ta 2016 ne Turkiyya ta kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan dakarun Kurdawa da kuma kungiyar IS, sai dai ba kasafai ake samun irin wadannan hare-haren da ake kaiwa mayakan gwamnatin Siriyan ba.

Idan har aka tabbatar da cewa dakarun gwamnatin na cikin wadanda aka kashe, harin zai kasance daya daga cikin mafi muni tun bayan tsamin danganatakar da ta kunno kai tsakanin kasashen biyu a shekarar 2020 bayan wani harin da gwamnatin Siriya ta kai wanda ya kashe sojojin Turkiyya 33 a lardin Idlib da ke arewa maso yammacin kasar.

Turkiyya ta zafafa kai hare-hare a yankunan da Kurdawa ke iko a Syria tun bayan wani taron kolin da aka gudanar a ranar 19 ga watan Yuli.

Kungiyar dakarun SDF, ta Kurdawan Syria, ta kirga a kalla  mutum 13 daga cikin mambobinta da aka kashe a hare-haren Turkiyya.

Turkiyya ta yi kakkausar suka ga shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad, inda ta ke marawa 'yan tawaye baya da suka yi kira da a kawar da shi tare da bude kofarta ga 'yan gudun hijira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.