Isa ga babban shafi

Ko Trump zai fuskanci tuhuma kan fitar da muhimman takardu daga White House ?

Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump na iya fuskantar tuhumar shari’a kan cire muhimman bayanan fadar shugaban kasar daga inda ake adana su, ciki harda da wasu takardu da ke dauke da manyan sirrin fadar White House zuwa gidansa da ke Mar-a-Lago na Florida

Tsohon shugaban kasar Amurka dake fuskantar binciken FBI. 12/08/22.
Tsohon shugaban kasar Amurka dake fuskantar binciken FBI. 12/08/22. REUTERS - DAVID DEE DELGADO
Talla

Menene sammacin binciken ya bayyana?

Sanarwar da hukumar binciken farin kaya na Amurka FBI ta fitar kan binciken gidan Trump dake Mar-a-Lago da ma'aikatar shari'a ta bayyana a ranar Juma'a ya nuna cewa jami'an tsaro na binciken Trump kan wasu manyan laifuffuka guda uku: ciki harda satar bayanan sirrin gwamnati, wanda ke da yiwuwar keta dokar leƙen asiri, wanda zai iya haɗawa da boye takardun da suka shafi tsaron ƙasa bisa buƙatar fallasa su ko batar da waɗannan bayanai.

Wasu bayanai daga wata kotun tarayya dake Florida da aka fitar ranar Juma'a, sun cewa jami’an FBI da suka binciki gidan Trump a Mar-a-Lago sun samu wasu takardun sirri har guda 11, ciki har da wasu da aka makawa "Babban Sirrin".

An dauki hoton rasidin kadarorin da aka samu a lokacin aiwatar da sammacin binciken da hukumar FBI ta yi a gidan tsohon shugaban kasar Donald Trump na Mar-a-Lago a Palm Beach, Fla., a ranar Juma'a, 12 ga Agusta, 2022. (AP Photo/Jon) Elswick)
An dauki hoton rasidin kadarorin da aka samu a lokacin aiwatar da sammacin binciken da hukumar FBI ta yi a gidan tsohon shugaban kasar Donald Trump na Mar-a-Lago a Palm Beach, Fla., a ranar Juma'a, 12 ga Agusta, 2022. (AP Photo/Jon) Elswick) AP - Jon Elswick

Nukilya

Jaridar Washington Post ta ruwaito cewa, har ila yau, jami'an na FBI na binciken wasu takardu da ke da alaka da makamin nukiliya a gidan na Trump dake Florida.

Da yake maida martani kan matakin ta shafin sada zumunta ranar Jumma’a mista Trump yace "batun makamin nukiliya" kage ne." Ya ce yana ba da hadin kai ga hukumomi a binciken da suk yi wanda ya kira amtsayin siyasa ce kawai, kuma bai dace ba.

Wadanne dokoki ne Trump ya karya?

Sammacin ya bai wa masu gabatar da kara damar ƙwace bayanan da ke ɗauke da shaida da suka saba wa dokokin tarayya guda uku, wato ta 18 USC 793 da 2071 da kuma 1519, wadanda ke bayani kan kaucewa amfani da bayanan gwamnatin tarayya a yanayin da bai kamata ba.

Kuma jerin takardun da jami’an FBI suka gano a gidan na Mar-a-Lago na da alaka da wadannan dokoki uku.

 

Jami'an hukumar FIB na Amurka lokacin da tunawa da harin 11 ga watan Satumba.
Jami'an hukumar FIB na Amurka lokacin da tunawa da harin 11 ga watan Satumba. REUTERS - JEENAH MOON

 

Dokar mai lamba 793 ta hana mallakar bayanan tsaron ƙasa ba tare da izini ba. Kuma ana iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekaru 10 a gidan yari kan kowane laifi. Dokar na ƙarƙashin Dokar Leken asiri ta 1917.

Sauran dokokin, 2071 da 1519, sun haramta ɓoye ko lalata takaddun gwamnati. Ana iya daurin tsakanin shekaru uku zuwa 20 a gidan yari.

Har ila yau, dokar tarraya ta haramta ɗaukar takaddun sirri da gangan zuwa wani wuri na daban ba tare da izini ba, amma dokar ba ta cikin ukun da aka ambata a cikin sammacin binciken.

Ko dara zata ci gida?

A shekarar 2018 ne Trump ya rattaba hannu kan wani sauyi a dokar da ya mayar da laifin karkatar da wasu bayanan sirri da kuma kara yawan zaman gidan yari ga mutanen da aka samu da laifin haka daga shekara daya zuwa biyar bayan sukar ‘yar takarar shugaban kasa a jam’iyyar Democrat Hillary Clinton da  ta yi amfani da adireshin email din kanta wajen aike da muhimman bayanai lokacin tana mastayin sakatariyar harkokin waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.