Isa ga babban shafi

Al'ummar Rasha na cikin hadarin fuskantar haramcin shiga Turai

Jamhuriyar Czech da za ta karbi jagorancin EU na karba-karba ta bayyana cewa haramcin izinin shiga kasashen Turai ga ilahirin ‘yan Rasha shi ne takunkumi naga ba da za ta lafta kan kasar.

Wani yanki da Rasha ta ragargaza a Ukraine.
Wani yanki da Rasha ta ragargaza a Ukraine. AP
Talla

Ministan harkokin wajen Czech Jan Lipavsky cikin wata sanarwa da ya fitar kamae yadda kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito, ya ce haramcin bayar da biz aga ilahirin ‘yan Rasha da ke son shiga Turai shi ne takunkumi na gaba da yiwa kasar illa.

A cewar Lipavsky zai gabatar da kudirin gaban taron ministocin wajen kasashen EU a karshen watan da muke ciki na Agusta.

Sai dai a cewar ministan wajen na Czech takunkumin haramcin bizar ba zai shafi ‘yan kasar da ke shiga yawon bude ido cikin kasashen na EU ba.

A baya-bayan nan dai EU ta gabatar da sabbin takunkumai 6 kan Rasha duk dai dangane da yakin da kasar ke yi a makwabciyarta Ukrain.

Ko a jiya alhamis shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya bukaci Turai ta sanya haramcin shige da fice tsakanin nahiyar da al’ummar Rasha.

A cewar Zelensky kamata ya yi a ware Rasha a gefe su ci gaba da rayuwarsu a duniyarsu su kadai har zuwa lokacin da za su sauya halinsu.

Jamhuriyar Czech ce kasa ta farko da ta sanya haramcin bayar da biz aga ‘yan Rasga tun daga ranar 25 ga watan Fabarairu kwana guda bayan fara mamayar Moscow a Kiev, said ai har yanzu ‘yan kasar na ci gaba da kwarara Turai.

Da zarar dai ‘yan kasar ta Rasha sun tsallake shingen Schengen da baya bukatar biza kai tsaye suna iya shiga Turai ciki har da ‘yan leken asirin kasar a nahiyar a cewar ministan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.