Isa ga babban shafi

'Yan kasar Poland 12 sun mutu a wani hadarin mota a Croatia

Akalla mutane 12 ne ‘yan asalin kasar Poland suka mutu yayinda wasu 30 kuma suka jikkata a wani hadarin mota da ya faru kan babbar hanyar Zagreb da ke Arewacin Croatia.

Tuni Ofishin jakadancin Poland da ke Croatia ya tabbatar da mutuwar 'yan kasar 12.
Tuni Ofishin jakadancin Poland da ke Croatia ya tabbatar da mutuwar 'yan kasar 12. REUTERS/News 5
Talla

Ministan cikin gida Davor Bozinovic a wani taron manema labarai da ya kira a arewacin birnin Varadzin bayan faruwar hadarin ya ce mutum 11 suka mutu a lokacin faruwar hadarin yayinda wani guda ya kara mutuwa bayan isa asibiti.

Shugaban sashen bayar da agajin gaggawa na Croatia Maja Grba ya ce 18 cikin mutane 30 da suka jikkata a hadarin na cikin mawuyacin hali kuma suna samun kulawar gaggawa a asibiti.

Mr Grba ya bayyana cewa bayan samun rahoton hadarin nan ta ke aka aike da tawagar masu bayar da agajin gaggawa ta mutum 16 don kai dauki.

Ofishin jakadancin Poland da ke Croatia ya tabbatar da cewa ilahirin wadanda suka mutu a hadarin ‘yan kasar Poland ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.