Isa ga babban shafi

Najeriya: Mutane 30 sun kone kurmus a wani hadarin mota a hanyar Kaduna

Rahotanni daga Najeriya na cewa Mutane 30 ne suka kone kurmus yayin da wasu motoci uku suka yi taho-mu-gama a kan wata babbar hanya a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar, kamar yadda wani jami'in kiyaye haddura ya bayyana a ranar Juma'a.

Wani hadarin mota da ya hallaka mutane a Najeriya.
Wani hadarin mota da ya hallaka mutane a Najeriya. Daily Post
Talla

Wani jami’in hukumar kiyaye hadurra ta tarayya a gundumar Zariya Abdurrahman Yakasai ya bayyana cewa, hatsarin ya afku ne a ranar Alhamis din da ta gabata yayin da wasu motocin bas guda biyu da wata karamar mota suka yi karo da juna a kauyen Hawan Mai Mashi da ke kan babbar hanyar Kano Kaduna zuwa Abuja babban birnin kasar.

Yakasai ya shaidawa RFI-Hausa cewa, Motocin guda uku kama da wuta ne bayan sun yi karo da juna, inda mutane 30 suka kone kurmus.

Hakazalika wasu fasinjoji da dama sun jikkata a hadarin, in ji shi.

“Sauran fasinjojin sun samu munanan raunuka kuma jami’an mu sun kai su asibiti, inda ake kula da su,

” inji shi.

Yakasai ya dora alhakin hatsarin kan gudu da kuma tukin ganganci.

Yawaitan Hadurra

Hatsarin mota ya zama ruwan dare a kan titunan Najeriyar da ba su da kyau da kuma rashin mutunta dokokin hanya.

A watan Fabrairu, mutane 18 ne suka rasa rayukansu a lokacin da wata mota ta yi taho-mu-gama da wata bas din fasinja a arewa maso gabashin jihar Yobe.

A shekarar da ta gabata dai an samu hadurran kan tituna har sau 10,637 a Najeriya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 5,101 tare da raunata mutane 30,690, kamar yadda alkaluman hukumar kiyaye hadurra suka nuna.

Zaku iya latsa alamar sauti domin sauraron Abdurrahman Yakasai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.