Isa ga babban shafi
Najeriya-Ibadan

Hadarin mota ya hallaka mutane 14 a kan hanyar Lagos zuwa Ibadan

Wani Kazamin hadarin mota akan hanyar Lagos zuwa Ibadan da ke Najeriya ya yi sanadiyar mutuwar mutane 14 da suka kone kurmus.

Hadarin mota ba sabon abu ba ne a kan titunan Najeriya ta yadda mutane da dama kan rasa rayukansu a kowacce rana.
Hadarin mota ba sabon abu ba ne a kan titunan Najeriya ta yadda mutane da dama kan rasa rayukansu a kowacce rana. Reuters/Stringer
Talla

Rahotannin sun ce hadarin da aka yi da misalin karfe 10 da rabi na daren jiya ya ritsa da motoci guda 3 cikin su har da da motar safa da ke dauke da fasinjoji.

Mai magana da yawun hukumar kula da ka’idodin tuki Babatunde Akinbiyi ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar cikin mutanen 14 da suka mutu har da yara kanana guda 3 da ke cikin motar safar.

Jami’in ya ce fasinjoji 17 ke cikin motar lokacin da direbar ta ya yi kuskure wajen wuce wata mota, bai san cewar an aje wata mota da ta lalace a gefen hanya ba, abinda ya sa motar ta fadi ta kuma kama da wuta nan ta ke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.