Isa ga babban shafi
Kamaru

Hadarin mota ya hallaka sama da mutane 53 a Kamaru

Hukumomin Kamaru sun tabbatar da mutuwar mutane 53 da jikkatar wasu 29, sakamakon wani hadarin mota da ya auku da sanyin safiyar yau a yammacin kasar, bayan da Bus din safa-safa dauke da fasinjoji 70 yayi taho mu gama da mota dauke da man fetir.

Hadarin mota da ya hallaka sama da mutane 50 a kasar Kamaru
Hadarin mota da ya hallaka sama da mutane 50 a kasar Kamaru RFI Hausa
Talla

Gwamnan jihar Yamma Awa Fonka Augustine da ya ziyarci Dschang inda lamarin ya auku, yace an samu gawar mutane 53 da suka kone kurmus, yayin da aka kwantar da wadanda suka jikkata a asibiti.

A wani hawa da gangara ne dake titin da ya hada birnin Bafousam na Yammacin kasar zuwa Yaounde, inda ake kira Falaise hadarin ya auku da misali karfe 4 na asuba, inda shaidu suka ce, babbar motan da ke dauke da jarkunan man fetir dake fitowa daga Najeriya bashi da biriki.

Ana yawaitan samun hadduran mota a kasar Kamaru wanda so tari kan kai ga rasa rayuka, abin da masana ke danganta wa da rashin kyawun hanya da kuma gangancin direbobi da rashin cika ka`idojin bin hanya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.