Isa ga babban shafi
Najeriya

Hadarin mota ya hallaka dalibai 23 a Kano

Wani mummunan hadarin mota da ya afku akan hanyar Kano zuwa karamar hukumar Gaya da ke yankin arewacin Najeriya ya yi sanadin mutuwar wasu dalibai da malaman makarantar sakandare 23.

Hanyar ta Gaya zuwa Kano na shirin zama babban tarkon mutuwa yayinda mahukunta ke ci gaba da nuna halin ko'inkula kanta, duk da lakume rayukan al'umma da ta ke ci gaba da yi.
Hanyar ta Gaya zuwa Kano na shirin zama babban tarkon mutuwa yayinda mahukunta ke ci gaba da nuna halin ko'inkula kanta, duk da lakume rayukan al'umma da ta ke ci gaba da yi. REUTERS/Stringer
Talla

Hadarin dai ya auku ne sakamakon taho-mu-gama tsakanin motar daliban da kuma wata babbar motar Tanka, da tsakar ranar yau Talata.

Rahotanni sun ce daliban wadanda suka yo tattaki daga karamar sakandire ta Misau da ke jihar Bauchi sun je kanon ne da nufin ziyarar kara Ilimi tsakaninsu da takwarorinsu daliban jihar.

Tuni dai Rundunar 'Yansandan jihar Kanon ta bakin DSP Magaji Musa Majiya tabbatar da faruwar lamarin, inda tuni aka tafi ga gawakin daliban 20 da malamansu 2 da kuma direbansu guda jihar ta Bauchi.

Duk da cewa al'umma na korafi kan lalacewar hanyar ta Gaya zuwa Kano, amma Kakakin hukumar kiyaye afkuwar hadurra a Kanon Kabiru Daura ya alakanta hadarin da gudun ganganci da ya zargi direban daliban da aikatawa gabanin afkuwar hadarin.

Hanyar ta Gaya zuwa Kano na shirin zama babban tarkon mutuwa yayinda mahukunta ke ci gaba da nuna halin ko'inkula kanta, duk da lakume rayukan al'umma da ta ke ci gaba da yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.