Isa ga babban shafi

Duniya ta yi asarar Dala biliyan 72 saboda wasu bala'o'i

Wasu alkaluma da kamfanin Inshorar Switzerland ya fitar ya nuna yadda duniya ta yi asarar Dala biliyan 72 a watanni shidan farkon shekarar nan sakamakon bala’o’in da suka kunshi ambaliyar ruwa gobarar daji da sauransu.

Kasashen duniya sun yi asarar dukiya mai tarin waya saboda ambaliyar ruwa
Kasashen duniya sun yi asarar dukiya mai tarin waya saboda ambaliyar ruwa REUTERS/Kyodo
Talla

Wani rahoto da kamfanin inshorar na Switzerland Swiss Re ya fitar a wannan Talatar kan kiyasin adadin kudaden da duniya ta yi asara daga watan Janairu zuwa Yulin da ya gabata, ya ce alkaluman sun kusa daidai da yadda duniya ke gani kusan shekaru 10 a jere.

Sai dai jumullar asarar ta Dala biliyan 72 bai kai irin asarar da bala’o’in suka haddasa wa duniya fuskanta ba a watanni 6 farkon shekarar 202, amma ya yi kasa da asarar Dala biliyan 74 da ake ganin shekaru 10 da suka gabata.

Shugaban sashen bincike na kamfanin inshorar Swiss Re Martin Bertogg ya nuna yadda sauyin yanayi ya yi tasiri wajen haddasa bala’o’in musamman a Australia da Afrika ta Kudu, inda aka samu galibin ambaliyar ruwa da kuma tsawa mai karfi.

Kamfanin wanda ke Zurich da ke matsayin inshora ga kamfanonin Inshora na sassan duniya ya ce, hatta a Turai an samu asarar tarin dukiya sakamakon kakkarfar tsawar da yankuna da dama ke fuskanta hakazalika Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.