Isa ga babban shafi

An kashe kananan yara dubu 2 da 515 a tashe-tashen hankulan bara

Majalisaar Dinkin Duniya za ta gudanar da bincike game da kisa da kuma raunin da aka yi wa kananan yara a kasashen Ukraine da Habasha da Mozambique.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce, za su gudanar da bincike kan kisan da aka yi wa yara a kasashen Ukraine da Habasha da Mozambique.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce, za su gudanar da bincike kan kisan da aka yi wa yara a kasashen Ukraine da Habasha da Mozambique. AP - Theresa Wey
Talla

Babban Magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana haka a cikin wani sabon rahoto da aka fitar, wanda ya gano cewa, kananan yara dubu 2 da 515 ne aka kashe, sannan aka raunata dubu 5 da 555 sakamakon tashe-tashen hankulan da suka auku a bara.

Rahoton na shekara-shekara mai taken ‘kananan yara da rikici’  wanda aka wallafa a Litinin din nan, ya kuma tabbatar cewa, lallai yara dubu 6 da 310 ne aka tilasta musu taka rawa a yake-yaken da aka gani a bara a sassan duniya.

Kazalika rahoton ya kara da cewa, akwai wasu nau’ukan keta hakkokin yara da aka yi kamar sace su ko kuma lalata da su, baya ga kaddamar musu da farmaki a makarantu da asibitoci, sannan kuma aka ki ba su agajin gaggawaa a lokacin tashe-tashen hankulan.

Sai dai keta hakokin kananan yaran da aka tabbatar, ya fi kamari  a kasashen Yemen da Syria da Afghanisan da Jamhuriyar Demokuradiyar Congo da Somalia da Isra’ila da kuma yankin Falasdinu.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya ce, nan da shekara mai zuwa, za su bada tabbacin irin girman cin zarafin da aka yi wa kananan yaran a kasashen Ukraine da Habasah da Mozambique a saabon rahoto na gaba da za a saki a badi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.