Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 79 a Brazil
Akalla mutane 79 ne suka rasa rayukansu a Brazil sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka shatata, lamarin da ya yi sanadiyar bacewar gomman mutane kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.
Wallafawa ranar:
Yanzu haka masu aikin ceto na ci gaba da neman sauran mutane da watakila ke da nisan kwana, yayin da aka bayyana wannan ibtila’in na ambaliyar ruwa a matsayin mafi muni da kasaar ta gani a baya-bayan nan.
Adadin mutanen da lamarin ya rutsa da su ya karu sosai a karshen mako da suka hada da wadanda zabtarewar laka ta share su bayan ruwan saman ya haddasa tunbatsar wasu koguna a kasar.
Kawo yanzu, hukumomin kasar ba su bada cikakken bayani ba game da ainihin mutane da suka bace a sanadiyar musibar, amma da farko jami’an tsaron farin kaya na kasar sun ce, mutane 56 ne suka bace, yayin da kusan dubu 4 suka rasa gidajensu.
Gwamnan Pernambuco, Paulo Camara ya bayyana cewa, za a ci gaba da aikin ceto har sai an gano sauran mutanen da suka yi batan-dabo.
A bangare guda, masu hasashen yanayi sun ce, da yiwuwar a ci gaba da zabga ruwan sama kar da bakin kwaraya a wannan rana ta Litinin a kasar ta Brazil.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu