Isa ga babban shafi

Tax Justice Network ta zargi Amurka da taimakon batagari don kin biyan haraji

Wata Kungiyar da ake kira ’Tax Justice Network‘ a Birtaniya ta bayyana kasar Amurka a matsayin wadda tafi taimakawa attajiran duniya da gurbatattun 'yan siyasa wajen boye dukiyarsu daga hukumomin duniya.

Kungiyar ta Tax Justice Network ta ce Amurka na matsayin mafaka ga attajirai da batagarin 'yan siyasa da ke son kaucewa biyan haraji a kasashensu.
Kungiyar ta Tax Justice Network ta ce Amurka na matsayin mafaka ga attajirai da batagarin 'yan siyasa da ke son kaucewa biyan haraji a kasashensu. REUTERS/Kacper Pempel/Illustration
Talla

Rahotan kungiyar na wannan shekarar yace yayin da aka samu raguwar samun sahihan bayanai dangane da hada hadar kudade a duniya, kasashe 5 dake cikin kungiyar kasashen G7 da suka fi karfin tattalin arziki a duniya ke da hurumin rabin koma bayan da aka samu.

Wadannan kasashe sun hada da Amurka da Birtaniya da Japan da Jamus da kuma Italia.

Kungiyar ta bayyana cewar akalla Dala triliyan 10 irin wadannan attajirai suka boye a duniya, wanda ya ribanya daukaci takardun kudin Dalar Amurka da na euro da ake amfani da shi a fadin duniya.

Rahotan kungiyar ya zargi kasashen G7 da yiwa dokar bayyana kadarorin da jama’a suka mallaka zagon kasa wajen kare irin wadannan attajirai daga biyan haraji.

Alex Cobham, shugaban kungiyar yace yanzu haka a duniya ana kokarin kawar da shinge dake kare dukiyoyin da attajiran Rasha suka mallaka tare da masu kaucewa biyan haraji da baragurbin yan siyasa da kuma masu aikata manyan laifuffuka dake halarta kudaden haramun, amma kuma kasashen Amurka da Birtaniya da Jamus da Italia da kuma Japan na yiwa yunkurin zagon kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.