Isa ga babban shafi
IS-Ta'addanci

Kasashen da ke kawance a yaki da IS na taro a Morocco don dakile karfin kungiyar

Kasashen duniya da ke kawancen yaki da mayakan IS sun fara wani taro a Morocco domin nazari akan yadda za su hana masu ikrarin jihadi sake farfadowa a gabas ta tsakiya da yankin arewacin Afirka.

Duniya na cike da fargabar yiwuwar dawowar kungiyar IS.
Duniya na cike da fargabar yiwuwar dawowar kungiyar IS. AP - Jalaluddin Sekandar
Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da takwaran sa na Morocco Naseer Bourita ke jagorancin taron, wanda ya shafi wakilan kasashen da dama da su ke bangaren tsaro da kuma diflomasiyya.

Blinken wanda ya samu wakilcin Victoria Nuland saboda harbuwar da ya yi da cutar korona, ya ce a shirye su ke su murkushe mayakan da ke ikrarin jihadi masu amfani da sunan ISIS ko Daesh.

Nuland ta ce a shekarun da suka gabata kawancen kasashen ya samu nasarar murkushe mayakan a Iraqi da Syria, amma kuma yanzu haka suna ci gaba da barazana wajen sake farfadowa.

Ana saran kawancen ya tara kudin da ya kai Dala miliyan 700 domin tabbatar da zaman lafiya a yankunan kasar Iraqi da Syria wadanda aka kubutar da su daga wadannan mayaka.

Wannan taron ya na zuwa ne shekaru 3 bayan samun nasarar kawar da Daular IS a Iraqi da Syria, yayinda mayakan ke kokarin kafa sansanoni a yankin sahel da Afirka ta Yamma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.