Turkiyya ta cafke wani barde na kungiyar IS
Rahotanni daga Turkiya sun ce ‘yan Sandan kasar sun yi nasarar kama wani babban jami’in kungiyar IS da ake danganta shi da zama hannun daman shugaban kungiyar Abubakar al-Baghdadi da aka kashe a shekarar 2019.
Wallafawa ranar:
Jami’an Yan Sandan sun bayyana mutumin dan kasar Afghanistan da ake yiwa lakabi da Basim cewar an kama shi ne lokacin wani samamen hadin kai da jami’an leken asirin kasar a Yankin Atesehir.
Kafofin yada labaran Turkiya sun ce mutumin da aka kama ya taimakawa Baghdadi buya a Idlib lokacin da ake neman sa ruwa a jallo.
Dan ta'addar ya shiga Turkiyya ne a watan Afrilu
Shi dai wanda ake tuhumar ya isa birnin Istanbul ne a ranar 28 ga watan afrilun da ya gabata da fasfo na jabu, kamar dai yadda tashar talabijin ta DHA News ta bayyana.
Tutkiyya ta kaddamar da farautar 'yan ta'adda musamman magoya bayan kungiyar IS sakamakon yadda suke kai hare-hare a cikin kasar, ciki har da wani hari da magoya bayan kungiyar suka kai a wani gidan rawa shekara ra 2017.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu