Isa ga babban shafi
Rasha - uKRAINE

Ukraine ta sake lalata wani jirgin ruwan yakin Rasha a Tekun Black Sea

Ukraine tace yau asabar ta sake lalata wani jirgin ruwan yakin Rasha kusa da tsibirin Snake na tekun Black Sea, inda aka jinjinawa sojojin Ukraine bisa jarumtakar da suka nuna wajen fatali da bukatar Rasha na mika wuya.

Wani maganadisu da ke wakiltar jirgin Rasha Moskva da ya nutse a cikin Tekun Bahar, Afrilu 14, 2022. Hoton da aka ɗauka a Sevastopol, Afrilu 15, 2022.
Wani maganadisu da ke wakiltar jirgin Rasha Moskva da ya nutse a cikin Tekun Bahar, Afrilu 14, 2022. Hoton da aka ɗauka a Sevastopol, Afrilu 15, 2022. © ALEXEY PAVLISHAK/REUTERS
Talla

Ma'aikatar tsaron Ukraine a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce wani jirgin mara matuki dauke da makami ya lalata jirgin Rasha mai ajin Serna da kuma na'urar kariya ta makamai masu linzami a karamin tsibiri da ke karkashin ikon Rasha.

Rasha ta ci gaba da luguden wuta

Hakan na zuwa ne yayin da Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta ce ta lalata wasu tarin kayan yaki da Amurka da kasashen Turai suka baiwa Ukraine a kusa da tashar jirgin kasa ta Bohodukhiv a yankin Kharkiv na kasar Ukraine.

Ma'aikatar ta ce ta kai farmaki kan wasu cibiyoyin sojin Ukraine 18 a cikin dare, ciki har da ma'ajiyar harsasai uku a Dachne, kusa da tashar jiragen ruwa na Odesa.

Kwashe fararen hula

Yayin da Ukraine ke fatan kwashe karin fararen hula daga masana'antar sarrafa karafa ta Mariupol da aka yi wa kawanya a daidai lokacin da sojojin Rasha suka kaddamar da hare-haren bama-bamai a duk fadin kasar gabanin bukukuwan ranar nasara a birnin Moscow.

Kamfanin sarrafa ƙarafa na Azovstal shi ne tingan ƙarshe na juriyar Ukraine da ke cikin birni mai tashar jiragen ruwa.

Ministan tsaron Ukraine ya ce dakarun Rasha sun sake kai farmaki a wurin, duk da cewa Rasha ta sanar tsagaita bude wuta domin barin baiwa fararen hula da suka makale damar ficewa daga rukunin.

Mataimakin Firayim Minista Iryna Vereshchuk ya ce masu aikin ceto za su yi kokarin kwashe karin fararen hula a ranar Asabar.

Bukin nasarar yakin duniya

A ranar Litinin ne Moscow da shugaban kasar Vladimir Putin za su yi bikin murnar nasarar yakin duniya na biyu da Tarayyar Soviet ta yi kan 'yan Nazi a Jamus tare da faretin ranar nasara na al'ada.

Yakin da Rasha ke yi a Ukraine ya fuskanci turjiya mai tsauri -- kuma ya tunzura kawayen Kyiv na yammacin kasar wajen kakaba mata takunkumin karya tattalin arziki Rasha da kuma ga Putin da makusantar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.