Isa ga babban shafi

Sama da kashi 21 na nau'ikan halittu masu jan-ciki na cikin hatsarin bacewa

Akalla kashi 21 na dabbobin da ke jan-ciki na fuskantar gagarumar baranazar bacewa daga doran duniya  da suka hada da kada da kunkuru.

Wasu nau'ikan Kadangare a tsibirin Galapagos da ke kasar Ecuador, 16 ga Janairun shekarar 2022.
Wasu nau'ikan Kadangare a tsibirin Galapagos da ke kasar Ecuador, 16 ga Janairun shekarar 2022. REUTERS - SANTIAGO ARCOS
Talla

Matsalar bacewar wasu nau’ukan halittu da tsirrai na ci gaba da kamari a sassan duniya, abin da ake kallo a matsayin babbar barazana ga doran duniyar da muke rayuwa a cikinta musamman ma ganin yadda hakan ke da nasaba da sauyin yanayi.

An tattara bayanai masu fadi a baya-bayan nan da ke nuna irin gagarumar barazanar da dabbibi masu jan-ciki ke ciki, inda aka ce kashi 40 na dabbobin da ke rayuwa a wuri mai danshi na cikin barazanar bacewa, baya ga wani kashi 13 na  wasu nau’ukan tsuntsaye.

A can baya dai, masu bincike sun gaza tantance ainihin adadin dabbobi masu jan-ciki da ka fuskantar barazanar bacewa daga doran duniya.

Yanzu haka masu binciken a cikin wani sabon rahoto da aka wallafa a mujallar Nature, sun ce, akwai kimanin nau’ukan dabbobi masu jan-ciki dubu 10 da 196 da za su iya bacewa nan gaba.

Daga cikin wannan adadin, sun gano cewa, akalla dubu 1 da 829, wato kashi 21 kenan, na cikin matsananciyar barazanar bacewar, kuma daga cikinsu har da kada da kunkuru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.