Isa ga babban shafi
Sauyin yanayi

An matsa kaimi irinsa na farko kan magance sauyin yanayi

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, an matsa kaimi irinsa na farko a tarihi wajen yaki da matsalar sauyin yanayi a daidai lokacin da kasashen duniya kimanin 200 suka gudanar da taro tare da amincewa da wani rahoton kwararru domin magance matsalar.

Wannan hoton na dauke da takaitaccen bayani kan yadda sauyin yanayi ya yi wa duniya lahani
Wannan hoton na dauke da takaitaccen bayani kan yadda sauyin yanayi ya yi wa duniya lahani Gal ROMA AFP
Talla

Shugaban Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya mai yaki da matsalar sauyin yanayi, Chair Hoesung Lee ya ce, ba a taba ganin jajircewa makamanciyar ta baya-bayan nan  ba wajen yaki da dumamar yanayi.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar wasu tarin matsaloli masu nasaba da sauyin yanayi kamar bacewar wasu nau’ukan halittu daga doran-kasa da lalacewar zamantakewa tsakanin tsirrai da muhalli da tsanantar cutakan da sauro ke yadawa da tsananin zafi da karancin ruwa baya ga kankancewar albarkatun gona.

A bara kadai, duniya ta gamu da jerin musibun ambaliyar ruwa mafi muni a tarihi, gami da matsanancin zafi da barkewar wutar daji  a nahiyoyi hudu na duniya.

Rahoton kwararrun na Majalisar Dinkin Duniya ya ce, dukkanin matsalolin da sauyin yanayin ya haddasa, za su ta’azzara nan da wasu gomman shekaru masu zuwa,  koda kuwa an shawo kan matsalar hayaki mai gurbata muhalli.

Nan da ranar 28 ga wannan wata na Fabairu, ake sa ran wallafa rahoton kwararrun mai dubban shafuka da ya kunshi shawarwarin magance matsalar ta sauyin yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.