Isa ga babban shafi
Iran-Nukiliya

Amurka za ta yi tirjiya ga kokarin ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran- Malley

Babban mai shiga tsakani daga bangaren Amurka a kokarin ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran Robert Malley ya ce kasar na shirin yin tirjiya ga ci gaban tattaunawar yarjejeniyar matukar ba ta saki wasu fursunoninta da ta ke tsare da su ba.

Babban mai shiga tsakani kan tattaunawar Amurka a kokarin ceto yarjejeniyar nukiloiyar Iran Robert Malley.
Babban mai shiga tsakani kan tattaunawar Amurka a kokarin ceto yarjejeniyar nukiloiyar Iran Robert Malley. Mazen Mahdi AFP
Talla

Washington ta tsaya kai da fata wajen ganin lallai Iran ta saki wasu Amurkawa 4 da ta ke tsare da su matukar ta na bukatar ci gaban tattaunawar don ceto yarjejeniyar.

A cewar Robert Malley duk da cewa batun yarjejeniyar Nukiliyar da kuma bukatar sakin mutanen da ke tsawon lokaci batutuwa ne mabanbanta amma suna fatan cimma su a lokaci guda.

A wata zantawarsa da Reuters, babban mai shiga tsakanin na Amurka Robert Malley ya ce abu ne mai wuya su iya sakin jiki a gyatta yarjejeniyar alhalin suna da mutanensu har guda 4 da Iran ke tsare da su.

Mr Malley ya ce tattaunawar bukatar dawo da yarjejeniyar na tafiya a bangare guda wata daban kan bukatar sakin mutanen 4 itama na tafiya da nufin cimma nasara a dukkaninsu.

A shekarun baya-bayan nan Iran ta kame ‘yan kasashen waje da dama kan laifukan leken asiri ko kuma batutuwa na tsaro duk da cewa ta musanta ikirarin kasashen yamma na sanya siyasa cikin kamen.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam na zargin Tehran da kokarin kame 'yan kasashen waje don samun fansar diflomasiyya daga kasashensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.