Isa ga babban shafi
Sauyin Yanayi

Duniya ta yi matukar zafi cikin shekaru 7 da suka gabata

Hukumar Kula da Yanayi ta Tarayyar Turai ta fitar da wani rahoto da ke cewa, shekaru bakwai da suka gabata, sun kasance mafi zafi a duniya, sakamakon karuwar sinadarin Methane a sararin samaniya, wanda ke kara yawan matsalar dumamar yanayi.

Kwararru sun ce, duniya ta yi zafi sosai a cikin shekaru 7 da suka gabata.
Kwararru sun ce, duniya ta yi zafi sosai a cikin shekaru 7 da suka gabata. GETTY/AFP/File
Talla

A cikin sabon rohotonta na shekara-shekara, cibiyar kula da yanayin ta Turai ta tabbatar da cewa shekarar 2021 ta shiga cikin jerin shekarun da aka fi fama da dumamar yanayi tun daga 2015.

Kazalika binciken masanan ya kuma gano an samu karin dumamar yanayi da akalla maki 1.1 zuwa maki 1.2 a ma’aunin Celcius, fiye da yanayin da duniya ta gani kafin samun ci gaban kafuwar masana'antu a tsakanin shekarun 1850 zuwa 1900 daidai.

Hukumomin kasashe a duniya dai na fuskantar caccaka daga kwararru musamman ma masu fafutukar kare muhalli da yaki da suyin yanayi, sakamakon karuwar bala'o'i masu alaka da dumamar yanayi da suka hada da munin iftila’in gobarar daji a kasashe da dama ciki har da Australia da kuma guguwa dauke da ruwan sama mai karfin gaske da ya haddasa ambaliya a sassan Asiya da Afirka da Amurka da kuma Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.