Isa ga babban shafi
Coronavirus

Yawan wadanda suka kamu da Korona ya zarce mutane miliyan 300

Adadin mutanen da suka kamu da cutar Korona a fadin duniya ya zarta miliyan 300, kamar yadda alkaluman hukumomin lafiya suka nuna a ranar Juma'a.

Wani bangare na taswirar Duniya da ke nuna barkewar cutar Korona.
Wani bangare na taswirar Duniya da ke nuna barkewar cutar Korona. Getty Images - da-kuk
Talla

Sabuwar kididdigar na zuwa ne,  a daidai lokacin da sabon nau’in cutar Koronar na Omicron ya haifar da hauhawar wadanda annobar ke harba inda aka ga karuwar yawansu mafi tsanani a duk rana cikin gwamman kasashe.

A cikin kwanaki bakwai da suka gabata dai, akalla kasashe 34 ne suka ba da rahoton gano adadin masu kamuwa da Korona mafi yawa, yanayi mafi tsanani da suka gani tun bayan barkewar annobar a shekarar 2020.

Daga cikin kasashen da suka fuskanci hauhawar ta masu Korona 18 na Turai, yayin da 7 ke nahiyar Afirka, kamar yadda alkaluman da kamfanin dillancin labarai na AFP ya tattara daga hukumomi.

A karshen makon nan shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi gargadin cewa bai kamata a sanya Omicron cikin nau’in Korona marar tsanani ba, domin kuwa yana kwantar da mutane a asibiti gami da kashe wasu da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.