Isa ga babban shafi
Duniya

An yi asarar Dala biliyan 170 saboda bala'o'i na duniya

Wata kungiya da ke bada taimako da yunkurin tsamo jama’a daga halin kunci a duniya ta ce an yi asarar da ta kai ta Dala biliyan 170 dai-dai da Yuro biliyan 150 sakamakon bala’o’in da suka faru, masu nasaba da sauyin yanayi a bana kadai a sassan duniya.

Daga cikin bala'o'in da suka addabi duniya har da ambaliyar ruwa
Daga cikin bala'o'in da suka addabi duniya har da ambaliyar ruwa AP - Delmer Martinez
Talla

Kungiyar ta bayyana hakan ne ta cikin wani rahoton shekara-shekara da ta saba fitarwa, inda ta ce a bana an sami karin Dala Biliyan ashirin, na asarar da duniya ta yi idan aka kwatanta da asarar da aka samu sakamakon sauyin yanayi a bara.

Bisa al’ada dai wannan kungiya kan mayar da hankali wajen tattara bayanai da asarar da aka samu sakamakon sauyin yanayi ko tashin Gobara, ambaliyar ruwa da kuma mahaukaciyar guguwa.

A cewar kungiyar a bara duniya ta yi asarar Dala biliyan 150, abin da ke nufin an sami karin kaso 13 cikin dari na asarar da aka tafka.

Kungiyar ta ce, abin takaicin kuma shine yadda ake ci gaba da samun karin afkuwar bala’o’i wadanda dan adam ke haddasa su, ta hanyar sakaci ko kuma yiwa juna keta, al’amarin da a yanzu haka ke yiwa duniya barazana.

Kungiyar ta kara da cewa irin wannan tashe-tashen hankula sun raba hallaka mutane sama da dubu daya da 75 yayin da sama da miliyan daya da dubu dari uku suka rasa muhallan su.

Kungiyar ta ce mahaukaciyar guguwar Ida itace ta fi yin barna a banan, inda ta janyowa duniya asarar dala biliyan 65.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.