Isa ga babban shafi
australiya - zanga zanga

An gudanar da zanga-zangar adawa da rigakafin korona a Austiraliya

Dubban masu zanga-zangar da ke adawa da tilasta allurar rigakafin korona Australia sun fantsama titunan biranen kasar, yayin da a bangare daya wasu tsiraru dake goyan bayan matakan kiwon lafiyar su ma suka yi gangamin.

Dubban mutane sun gudanar da zanga-zangar adawa da allurar rigakafin korona a Australiya, 20/11/21.
Dubban mutane sun gudanar da zanga-zangar adawa da allurar rigakafin korona a Australiya, 20/11/21. William WEST AFP
Talla

Har yanzu hukumomin Australia basu tilasta karbar rigakafin Korona ba, kuma Shirin na samun nasara sosai, inda kusan kashi 85 na al'ummarta suka karbi cikakkiyar allurar rigakafin, kuma wadanda suka karbi allurar sau biyu na samun walwa kwarai.

To sai dai masu adawa ta matakin sun gudanar da zanga-zanga a wannan Asabar a manyan biranen Australiya da dama kan ka'idojin rigakafin, wadanda hukumomi suka daura su kan dai-dai kun ayyuka.

'Yan sanda sun ce kimanin mutane 10,000 ne suka taru a Sydney, inda wani mai zanga-zangar yayi shige mai kama da na dan gwagwarmayar 'yancin walwala dan kasar Scotland William Wallace a cikin fim din "Braveheart" yayin da wani ya yi jawabi sanye da kayan ado kamar na tsohon shugaban Amurka Donald Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.