Isa ga babban shafi
Makamashi

Karancin iskar gas ya fara gigita al'ummar duniya

Karancin makamashi a duniya da kuma tsadarsa na ci gaba da ta’azzara a sassan duniya, wanda kuma har ya fara sanya fargaba a zukatan jama’a musamman masu yunkurin zuwa hutu tsakanin China zuwa London yayin da ake tunkarar lokacin sanyi.

Wata cibiyar sarrafa iskar gas
Wata cibiyar sarrafa iskar gas Joe KLAMAR AFP/File
Talla

A yanzu haka, tsadar iskar gas na ci gaba da addabar kasashen duniya wadda har ta fara shafar ayyukan kamfanoni da ma’aikatu tsakanin manyan kasashen duniya.

Bala’in karancin gas din na kara gigita jama’a ne musamman a lokacin da kowanne yanki na duniya ke fuskantar sauyin yanayi, inda yake bazara a yankin Asia da arewacin Amurka.

Kasashen Tarayyar Turai ne suka fi dandana tsadar farashin iskar gas din, wadda kuma ake ganin ta shafi tashin farashin man fetur.

Karancin iskar Gas din dai ya tilasta wa wasu kasashen Turai irin su Burtaniya komawa ga habbaka kamfanonin samar da gawayi, duk kuwa da kiraye-kirayen da ake yi na sassauta amfani da shi saboda matsalar sauyin yanayi.

Baya ga Birtaniya, China da India ma sun rungumi batun habbaka Coal da nufin tunkarar tsadar iskar gas din, don sassauta samar da makamashi ga al’ummarsu.

Batun karanci da kuma tsadar iskar gas din na shafar ayyukan kasuwanci musamman a Jamus da Spain, abin da kai tsaye ke shafar tattalin arzikin kasashen. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.