Isa ga babban shafi
Canada - China

China ta saki 'yan Canada 2 da ta tsare tun shekarar 2018

Firaministan Canada Justin Trudeau ya ce hukumomin China sun saki wasu ‘yan kasar ta Canada 2 da suka tsare a gidan Yari tun shekarar 2018, bisa zargin su leken asiri, kuma tuni suka fice daga kasar a ranar Juma’a.

Firaministan Canada Justin Trudeau.
Firaministan Canada Justin Trudeau. Andrej Ivanov AFP/File
Talla

Trudeau ya ba da sanarwar ta ranar Juma'a ce sa'o'i bayan da hukumomin Amurka suka janye tuhumar da suke yi wa babbar jami’ar kamfanin sadarwar China na Huawei, Meng Wanzhou.

Matakan na ranar Juma’a da suka shafi manyan kasashen duniya dai, sun kawo karshen rikicin diflomasiyar da ya raunana dangantaka tsakanin Amurka da Canada, da kuma China a gefe guda cikin shekaru ukun da suka gabata.

Meng Wanzhou, babbar jami'ar kula da hada-hadar kudaden kamfanin sadarwar Huawei.
Meng Wanzhou, babbar jami'ar kula da hada-hadar kudaden kamfanin sadarwar Huawei. AP - DARRYL DYCK

Matakin farko na warware rikicin diflomasiyar ya zo ne da yammacin Juma'a lokacin da Amurka ta janye tuhume-tuhumen laifukan almundahanar da take yi wa Meng Wanzhou, babbar jami'ar kula da hada-hadar kudaden kamfanin sadarwar Huawei, wadda kuma 'ya ce wanda ya kafa kamfanin.

Kimanin awa guda bayan da jirgin Meng ya bar Canada zuwa China, Trudeau ya bayyana cewa ‘yan kasar ta Canada Michael Kovrig da Michael Spavor suka kama hanyar komawa gida daga China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.