Isa ga babban shafi
Amurka-China

Wanzhou ta gabatar da hujjoji don kare kanta

A kokarin da take na ganin cewa ba a tasa keyarta zuwa Amurka don ta fuskanci shari’a ba, babbar jami’ar kamfanin Huawei na kasar China da yanzu haka ke tsare a kasar Canada, ta kammala gabatar da hujjoji a gaban kotu.

 Meng Wanzhou
Meng Wanzhou © AFP
Talla

Tun da fari dai, an kama babbar jami’ar kamfanin, Meng Wanzhou sama da kwanaki dubu daya da suka gabata a kasar Canada bisa zargin ta da aikata laifukan da suka shafi kudi.

Da ma  Amurka ta dade da zargin matar da hada kai da ‘yar mamallakin kamfanin na Huawei Ren Zhengfei da hannu wajen damfarar wani bankin kasuwanci wajen ba su wasu  lambobin sirri na bogi, da aka yi amfani da su wajen sayar wa da kasar Iran wayoyin hannu.

A cewar sashen shari’a na kasar Amurkar, wannan dalili ya kusa jefa bankin cikin hadarin take dokar takunkumin tattalin arzikin da Amurkar ta kakaba wa Iran, da kuma batun amfani da Dalar Amurka wajen cinikayya da kamfanin na Huawei.

Wannan ce ta sanya Amurka ta bukaci Canada ta mika mata matar bayan ta kamata ta, don ta fuskanci shari’ar zargin da ake yi mata, amma matar ta shigar da kara kotu tana bukatar a dakatar da hukumomin Canada daga mikata zuwa Amurka.

Ya zuwa yanzu dai alkalin kotun da ke sauraren shari’ar Heather Holmes ya ce, ya kammala sauraren hujojjin dukannin bangarorin biyu, kuma ya sanya rana 21 ga watan Octoba don yanke hukunci kan mika matar ga Amurka don fuskantar hukunci ko kuma akasin hakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.