Isa ga babban shafi
IS-Faransa

Takaitaccen tarihin Abu Walid Adnan al-Sharawi da Faransa ta kashe

Dakarun Sojin Faransa sun yi nasarar hallaka jagoran kungiyar IS a yammacin saharar Afrika, Adnan Abu Walid al-Sahrawi, dan ta’addan da Amurka ke nema ruwa a jallo bayan jagorantar harin da ya hallaka Sojinta.

 Adnan Abu Walid al Sahraoui.
Adnan Abu Walid al Sahraoui. - -/AFP/Archivos
Talla

Jagoran kungiyar ta IS a yammacin saharar Afrika, da aka fi sani da Adnan Abu Walid al-sahrawi, asalin sunansa shi ne Lehbib Ould Ali Ould Said Ould Yumani kuma an haifeshi a garin Laayoune na Algeria ranar 16 ga watan Fabarairun 1973 daga cikin zurriyar ‘yan kasuwa mawadata wadanda daga baya suka koma rayuwa a sansanin ‘yan gudun hijira a cikin kasar, dalili kenan da ya sanya shi tasowa da tunani irin na ‘yan awaren Polisario ko kuma masu fafutukar ‘yantar da yammacin saharar Afrika, inda ya samu horo a hannun mayakan kungiyar.

Duk da cewa yayi zurfin karatu a bangaren kimiyya, a shekarar 1998 ya zama mamba a haddiyar kungiyar matasan sahara ta Sahrawi Youth Union gabanin hadewa da manyan kungiyoyin ta’addanci na yammacin Afrika kuma rawar ganinshi ta bashi damar shugabancin kungiyar IS a yankin.

La’akari da yadda al-Sahrawi ya yi kaurin suna wajen kai muggan hare-hare kan Soji da fararen hula kama daga na yankin da kuma Sojin ketare, hakan ya sanya shi kaurin suna ta zama cikin jerin ‘yan ta’addan da kasashen Duniya ke nema ruwa a jallo.

Jagoran na IS gabanin kisan shi a farmakin na dakarun Faransa, ya yi mulki da takalmin karfe hatta tsakanin mutanen da ke biyayya ga mulkinsa, inda ya ke yanke hannun duk wanda aka samu da laifin sata ko kuma fille kai, ko yin yankan rago ga wadanda aka samu da aikata ba dai dai ba duk dai da sunan tabbatar da dokokin addini.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.