Isa ga babban shafi
Amurka-China

Za mu tsaurara matsin lamba kan China-Amurka

Mataimakiyar shugaba Joe Biden,  Kamala Harris ta ce Amurka za ta tsara sabbin hanyoyin kara matsin lamba kan China, wadda ta zarga da danne hakkokin kasashen nahiyar Asiya da ta yi iyaka da su ta ruwa.

Kamala Harris a Vietnam
Kamala Harris a Vietnam REUTERS - EVELYN HOCKSTEIN
Talla

Harris ta caccaki China ne a kasar Vietnam yayin ziyarar da ta fara zuwa wasu kasashen Asiya domin karfafa alakar Amurka da su.

A yayin ganawarta da shugaban Vietnam Nguyen Xuan Phuc, Harris ta ce Amurka za ta ci gaba da kalubalantar fin-karfin da China ke yi wa kasashen Asiya wajen mamaye yankunansu na kan teku da ke kan iyakokinsu.

A yayin da ta ziyarci Singapore kuwa, mataimakiyar shugaban Amurkar ta zargi China da nuna fin karfi wajen tsoratar da makotanta domin mamaye yankunan ruwan tekun kudancin Sin masu arzikin albarkatun karkashin kasa.

Sai dai China ta mayar da martani kan zargin, inda ta tuhumi Amurka da munafurcin haddasa rikici tsakaninta da kasashen nahiyar Asiya, domin dakushe tasiri da kuma kimar da take da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.