China ta yanke hukunci kan Michael Spavor saboda samun sa da laifin leken asiri
Wata kotu a China ta yanke hukuncin daurin shekaru 11 a kan wani dan kasuwar Canada Michael Spavor saboda samun sa da laifin leken asiri, yayin da Canada ke cewa kage aka masa.
Wallafawa ranar:
Minti 1
Talla
A shekarar 2018 aka tsare Spavor tare da wani dan kasar Canada Michael Kovrig a shari’ar da kasar sa ke dangatawa da siyasa sakamakon kama shugabar kamfanin Huawei Meng Wanzhou saboda sammacin da Amurka ta gabatar.
Dangantaka tsakanin kasashen biyu tayi kamari, yayin da China ke zargin Canada da sanya siyasa a cikin harkokin da suka shafi shari’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu