Isa ga babban shafi
Faransa - Isra'ila

Pegasus: Macron ya bukaci Isra'ila ta dauki mataki kan manhajar leken asiri

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kira Firayin Ministan Isra’ila Naftali Bennett ta wayar tarho don nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa an yi kutse a wayarsa ta Manhajar leken asiri na Isra’ila wato Pegasus.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. AP - John Thys
Talla

 

Rahotanni daga kafafan yada labaran Isra’ila na cewa, tattaunawar ta gudana ne a ranar Alhamis din da ta gabata kuma gidan talabijin na Isra’ila N12 ya bayyana shi.

A cewar kafafen yada labaran, Emmanuel Macron ya bukaci mahukuntan Isra’ila su dauki batun da mahimmanci, kuma su kwana da sanin cewa kasar Moroco ke amfani da manhajar da kamfanin NSO na Isra’ila ya kera.

A nasa bangare, FirayinMinista Isra’ila yace, tun kafi isowarsa gwamnati lamarin ya faru, kuma zai tura dawaga ta musamman karkashin jagorancin ministan tsaron kasar Benny Gantz zuwa Paris don yiwa shugaba Macron Karin haske.

Ba dai kasar Faransa kadai ta damu da wannan batu ba, domin kuwa jami’an gwamnatin Amurka sun tuntubi wata majiyar tsaro ta Isra’ila a ‘yan kwanakin nan don samun cikakken bayani kuma sun ce sun damu da bayanin da aka fitar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.