Isa ga babban shafi

Maroko ta yi barazanar daukar matakin shari’a kan masu zarginta da leken asiri

Mahukuntan kasar Maroko sun karyata zargin yin amfani manhanjar Pegasus da Isra’ila ta kera don yin leken asiri a wayoyin jama’a, tare da yin barazanar gurfanar da wadanda ke wannan zargi a gaban kotu. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar kare ‘yan jaridu ta duniya Reporters Sans Frontieres ta bukaci Isra’ila ta dakatar da sayar wa kasashe wannan manhanja, wadda bayanai ke cewa an yi amfani da ita don bibiyar wayoyin wasu shugabanni da kuma daruruwan ‘yan jaridu sassan duniya.

Wayar Salula dauke da manhajar leken asiri na Isra'ila.
Wayar Salula dauke da manhajar leken asiri na Isra'ila. AFP - JOEL SAGET
Talla

Shugaban kungiyar RSF mai cibiya a birnin Paris na kasar Faransa Chiristope Deloire cikin sanarwa ya yi kira ga Firayim Ministan Isra'ila Naftali Bennett da ya gaggauta dakatar da manhajar dake dauke da fasahar leken asirin har sai lokacin da aka samar da ka'idoji kariya.

Sama da wayoyi 50

Kiran kungiyar na zuwa ne bayan da aka bankodo kamfanin na Isra’ila NSO yi wa mutane kimanin dubu 50 leken asiri ta hanyar makala boyayyiyar manhaja a cikin wayoyinsu na salula, yayin da bayanai ke cewa, fitattun ‘yan jarida da masu gwagwarmaya da attajirai da ‘yan siyasa na cikin wadanda aka yi musu leken asirin.

Shugabannin da lamarin ya shafa

Jerin lambobin wayar salula da aka makalawa Manhajar mai suna “Pegasus” sun hada harda na shugabannin kasashen duniya 14 ciki harda da shugaban Faransa Emmanuel Macron da na Afirka ta Kudu Cyril Ramaposa, sai kuma sarkin Morocco Mohammed na VI.

Manhajar na kamfanin NSO da ‘yan jaridu suka bankado, na iya kutsawa cikin wayoyin salalu ba tare sanin masu shi ba, kana ta baiwa mai amfani da ita damar karanta sakonni da sanin inda mai wayar yake da kuma kunna kyamarar wayar makirhonta tare da tattaro bayanan da ke kunshe a cikin wayar ba tare da saninsa ba.

Tuni aka zargi kasar Morocco da amfani da mahanjar da Isra'ila ta kera wajen leken asirin wayoyin al'umma a duniya, zargin da kasar ta musanta dare da ikirarin daukar matakin shari'a kan masu zargin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.