Isa ga babban shafi
Duniya-Corona

Shirin covax ya samu karin alluran rigakafi miliyan 110 daga China

Shirin Covax ya sanar da samun karin alluran rigakafin Covid-19 miliyan 110 daga kamfanonin China na Sinovac da Sinopharm, alluran da za su taimaka wajen wadata matalautan kasashe da suka dogara ga shirin na Covax wajen yiwa al’ummarsu rigakafin.

Wasu alluran rigakafin covid-19 karkashin shirin Covax.
Wasu alluran rigakafin covid-19 karkashin shirin Covax. AFP - NHAC NGUYEN
Talla

Yarjejeniyar samar da alluran miliyan 110 da aka cimma tsakanin kamfanonin na China biyu da shirin na Covax wanda hadakar Gavi ke sanarwa yau litinin, ta ce zai amfani tsarin rabon alluran da ma kokarin yakar cutar dai dai lokacin da nau’in Delta ke ci gaba da barna a sassan Duniya.

Shugaban hadakar ta Gavi Seth Berkley da ke yabawa da matakin cimma yarjejeniyar, ya ce samun karin kamfanoni 2 zai taimaka wajen kammala samar da alluran da ake bukata a kan lokaci, kari kan kamfanoni da nau’ikan allurai 11 da yanzu haka shirin ke da shi ciki har da alluran AstraZeneca da Johnson and Johnson da Moderna da kuma Pfizer.

Gabanin kulla yarjejeniyar ta Covax da kamfanonin na China 2 wato Sinovac da Sinopharm sai da hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gwaji tare da tantance sahihancin allurar rigakafin inda ta sahale amfani da shi a yanayi na gaggawa.

Sanarwar da Gavi ta fitar, ta ruwaito Seth Berkley na cewa, nan da ‘yan lokaci kankani za a fara aikin raba alluran miliyan 110 ga kasashe don murkushe cutar wadda zuwa yanzu ta hallaka mutane fiye da miliyan 4.

Har yanzu dai shirin na Covax na ci gaba da neman tallafin kudaden sayen wadatattun alluran don taimakawa matalautan kasashe da kef ama da annobar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.