Kwamitin tsaro na MDD zai yi zama na musamman kan kisan shugaban Haiti
Kwamtin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana kaduwa a game da kisan shugaban kasar Haiti, Jovenal Moise, wanda aka bi shi har gida aka yiwa kisan gilla a Larabar nan.
Wallafawa ranar:
Mambobin kwamitin sun kuma bayyana damuwa kan halin da mai dakin shugaban, Martine Moise ke ciki bayan samun rauni sakamakon harbinta da bindiga da maharan suka yi a jiya.
Shugaban Amurka Joe Biden, wanda ya bayyana rashin jin dadinsa a game da wannan kisan gillar ya ce akwai bukatar karin bayani a game da al’amarin, a bangare guda, Firaministan Birtaniya Boris Johnson yayin bayyana kaduwarsa da kisan, ya yi kira da a kwantar da hankula a kasar ta Haiti, yana mai yi wa al’ummar kasar ta’aziyya.
Tarayyar Turai, ta bakin babbar jakadanta, Josep Borrell ta yi kashedin cewa kisan shugaba Jovenel Moise ka iya ta’azzarar tashin rikici a kasar ta yankin Caribean, tana mai cewa dole ne a kama tare da gurfanar da wadanda suka aikata aika aikar a gaban kuliya.
A Alhamis din nan kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya zai gudanar da wani taron gaggawa game da kisan shugaba Jovenal Moise, kamar yadda Amurka da Mexico, wadanda mambobin wucin gadi ne a kwamitin suka bukata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu