Isa ga babban shafi
Bakin haure

Bakin haure sun mutu a tekun Tunisia

Akalla bakin haure 21 ne suka mutu bayan kwale-kwalen da ke dauke da su ya nitse a gabar tekun Tunisia. Wani jami’in tsaro a yankin ya ce, wannan hatsarin jirgi shi ne irinsa na biyu cikin kwanaki biyu a yankin da ya auku.

Wasu 'yan ci rani yayin kokarin tsallaka ruwa don shiga tsibirin Cueta dake kasar Spain.
Wasu 'yan ci rani yayin kokarin tsallaka ruwa don shiga tsibirin Cueta dake kasar Spain. AP - Antonio Sempere
Talla

Kanar Houssem Ibebli daga hukumar tsaron kasar, ya ce masu gadin gabar tekun sun gano gawarwakin a tashar jirgin ruwa ta Sfax.

Rahotanni a ranar Asabar sun ce, akalla bakin haure 43 ne suka nitse a cikin jirgin yayin da aka ceto wasu 84 bayan da wani jirgin ruwa ya kife da shi a kusa da gabar tekun Tunisia na Zarzis.

Mahukunta sun ce bakin hauren na kokarin tsallaka Bahar Rum daga Libya zuwa Italiya.

Kamar yadda bayanai ke cewa, masu gadin gabar teku sun yi nasarar dakile ayyukan bakin haure 10 a cikin 'yan kwanakin nan tare da ceto bakin haure 158.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.