Isa ga babban shafi
Amurka-Birtaniya

Biden na ziyarar farko a Turai watanni 5 bayan fara shugabancin Amurka

A zangon farko na ziyarar da ya fara a Yankin Turai, a yau alhamis shugaban Amurka Joe Biden zai gana kai-tsaye da firaministan Birtaniya Boris Johnson, tare da bitar wata yarjejeniyar alaka tsakanin Amurka da Birtaniya, wadda tsoffin shugabannin kasashen biyu wato Winston Churchill da Franklin D. Roosevelt suka sanya wa hannu a 1941.

Shugaba Joe Biden na Amurka bayan isa birnin London a Birtaniya.
Shugaba Joe Biden na Amurka bayan isa birnin London a Birtaniya. © REUTERS - PHIL NOBLE
Talla

A yammacin jiya ne dai shugaba Biden ya isa Birtaniya ziyara ta farko a wata kasa ta waje watanni biyar da rantsar da shi a matsayin shugaban Amurka, inda zai tattauna da firaminista Johnson a Carbis Bay da ke matsayin wata cibiyar yawon bude ido a kudu maso yammacin Birtaniya.

A wannan gari ne shugabannin kasashe 7 masu karfin tattalin arziki a duniya za su gudanar da taronsu wanda zai fara daga gobe juma’a har zuwa ranar lahadi, inda shugabannin za su tattauna kan matsalar dumamar yanayi da kuma yadda za a farfado da tattalin arzikin duniya daga matsalolin covid-19.

Shugaba Biden zai kuma yi amfani da damar zuwan na sa Birtaniya wajen kai wa Sarauniyar Ingila Elizabeth II ziyarar girmamawa a daya daga cikin fadojinta da ke Windsor a ranar lahadi.

Wasu daga cikin jerin abubuwan da ke jiran shugaban na Amurka a wannan ziyara sun hada da halartar taron kungiyar tsaro ta Nato, sai kuma ganawa da shugabannin kasashen yankin Turai a Brussels, yayin da a ranar laraba mai mai zuwa zai gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a birnin Geneva. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.