Isa ga babban shafi
Biden-Korona

Biden ya kaddamar da shirin tallafa wa kasashe marasa karfi da rigakafin Korona

Shugaban Amurka Joe Biden ya kaddamar da shirin kasar na tallafawa Duniya da alluran rigakafin coronavirus miliyan 80 alluran da kashe 75 na yawansu zai tafi cikin shirin Covax.

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. AP - Evan Vucci
Talla

Sanarwar da fadar White House ta fitar, za a raba alluran ne ga kasashen da ke tsananin bukata don tallafawa a yaki da cutar ta Covid-19 wadda ke ci gaba da zama babbar barazana ga Duniya.

A cewar Biden, kamar yadda sanarwar ta ruwaito rabon alluran ba zai nuna fifiko ko kuma banbanci tsakanin kasashen da ke tsananin bukatarta ba musamman na latin Amurka da Caribbean da kuma Kudanci da kudu maso gabashin Asiya baya ga nahiyar Afrika.

Sanarwar ta fadar White House ta nuna cewa, Amurka za ta fitar da alluran miliyan 80 daga karshen watan Yuni, yayin da kashe 75 na jumullarsu za su tafi karkashin shirin Covax na hukumar Lafiya da Duniya, shirin da ke tabbatar da daidaito wajen rabon allurar musamman ga kasashe marasa karfi.

Matakin na Biden na zuwa duk da matsin lambar da ya ke fuskanta daga sassan gwamnatin kasar dangane da shirin na yin amfani da kaso mai yawa na alluran rigakafin kasar da nufin tallafa wa kasashen Duniya, duk da yadda kasar ke ci gaba da fuskantar na ta matsalolin a yaki da cutar ta Covid-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.