Isa ga babban shafi
Burkina Faso - Ta'addanci

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya harzuka da kisan fararen hula a B. Faso

Babban sakataren majalisar dinkin Duniya,  Antonio Guterres ya harzuka da kisan sama da fararen hula 120 a Burkina Faso ranar Asabar, a hare hare mafi muni tun da kasar ta fada rikicin mayaka masu ikirarin jihadi a shekarar 2015.

Sakataren Malisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakataren Malisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. Michael Sohn POOL/AFP/File
Talla

A wata sanarwa da ta samu sa hannun kakakinsa, Stephane Dujarric, Guterres ya bayyana bacin ransa a game da kashe kashen daruruwan farar hula da suka hada da mata da yara.

Gwamnatin Burkina Faso ta ce ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi sun kashe fararen hula masu mabambamtan shekaru har 138, kana suka cinna wa gidaje da kasuwa wuta a yankin da ke kusa da iyakokin Mali da Nijar.

Guterres ya caccaki wannan ta’asa, sannan ya jaddada bukatar kasashen duniya su rubanya goyon bayan da suke bai wa kasashen da ke fama da matsalar ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.