Isa ga babban shafi

Covax ya samu tallafin Dala biliyan 2 da rabi

Shirin Covax na taimakawa kasashe matalauta samun allurar rigakafin cutar korona yace ya samu taimakon kusan Dala biliyan 2 da rabi daga masu bada agaji na duniya domin cigaba da taimakawa kasashen dake bukatar maganin.

Samfurin maganin AstraZeneca
Samfurin maganin AstraZeneca REUTERS - DADO RUVIC
Talla

Shidai wannan shiri na kokarin ganin ya taimaka wajen baiwa akalla kashi 30 na mutanen dake kasashe 92 da suka fi fama da talauci a duniya maganin rigakafin da kuma kashi 20 a kasar India.

Sai dai duk da samun wannan taimako, shugabannin shirin na bayyana damuwa kan yadda zasu samu maganin a cikin lokaci daga kamfanonin dake sarrafa shi.

Seth Berkley, shugaban kungiyar Gavi alliance dake jagorancin shirin yace aikin su ya gamu da matsaloli sakamakon sake barkewar cutar a kasar India wanda yayi illa ga aikin samar da maganin a kasar.

Shirin Covax ya samar da allura miliyan 80 ga kasashe 127 kuma kashi 97 daga cikin allurer ya fito ne daga samfurin AstraZeneca.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.