Isa ga babban shafi
Coronavirus

Sama da mutane biliyan ɗaya da rabi sun karɓi alluran rigakafin korona a duniya

Watanni shida bayan fara amfani da maganin rigakafin cutar korona, ya zuwa yanzu an yiwa jama’a allurar da yawanta ya kai sama da biliyan guda da rabi a fadin duniya, kamar yadda alkaluma suka nuna.

Wata ma'aikaciyar jinya Janete Da Silva Oliveira yayin da take shirya allurar rigakafin Oxford-AstraZeneca a wani yankin na kasar Brazil 09 ga watan Fabrairu 2021.
Wata ma'aikaciyar jinya Janete Da Silva Oliveira yayin da take shirya allurar rigakafin Oxford-AstraZeneca a wani yankin na kasar Brazil 09 ga watan Fabrairu 2021. MICHAEL DANTAS AFP/File
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace ya zuwa karfe 3 da rabi na ranar Laraba, an yiwa mutane biliyan guda da miliyan 500 da dubu 17,337 allurar a kasashe 210 dake fadin duniya.

Alkaluman sun nuna cewar kusan kashi uku bisa biyar na wadanda suka karbi allurer sun fito ne daga kasashen China, wadda ta yiwa mutane kusan miliyan 421 allurar, sai Amurka mai mutane kusan miliyan 274 da rabi sannan India mai mutane kusan miliyan 184 da rabi.

Dangane da yawan mutanen da kowacce kasa ta yiwa allurar kuwa, Israila ke sahun gaba, ganin yadda ta yiwa kowadanne mutane 6 daga cikin 10 dake kasar ta, sai Birtaniya da ta yiwa kashi 54 na jama’ar kasar allurar sannan Bahrain da ta yiwa kashi 50 na jama’ar ta rigakafin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.